Gwamnati Nigeria ta ce ta tsaya tsayin daka kan matakin da ta dauka na soke takardar shaidar digiri 22,700 da 'yan Najeriya suka samu a wasu jami'o'in "karya" da ke makwabtaka da Togo da Jamhuriyar Benin. Ministan Ilimi Tahir Mamman, wanda ke cikin shirin Siyasa na Lahadi na gidan Talabijin na Channels, ya ce ‘yan Najeriya da suka samu shaidar digiri daga irin wadannan manyan makarantun “ba bisa ka’ida ba” suna bata sunan Najeriya.
Gwamnati Nigeria ta ce ta tsaya tsayin daka kan matakin da ta dauka na soke takardar shaidar digiri 22,700 da 'yan Najeriya suka samu a wasu jami'o'in "karya" da ke makwabtaka da Togo da Jamhuriyar Benin. Ministan Ilimi Tahir Mamman, wanda ke cikin shirin Siyasa na Lahadi na gidan Talabijin na Channels, ya ce ‘yan Najeriya da suka samu shaidar digiri daga irin wadannan manyan makarantun “ba bisa ka’ida ba” suna bata sunan Najeriya. Ya ce matakin soke takardar shaidar digiri na jami’o’in da ba bisa ka’ida ba a jamhuriyar Benin da Togo ba abu ne mai tsauri ba, domin mahukuntan kasashen yammacin Afirka da ke makwabtaka da kasashen Afirka ta Yamma sun ce makarantun da abin ya shafa na bogi ne. A shekarar da ta gabata ne wani dan jarida a boye ya yi bayani kan yadda ya samu digiri a wata jami’a a Jamhuriyar Benin cikin kasa da watanni biyu, kuma a haka aka tura shi aikin yi wa kasa hidima (NYSC). Bayan haka ne gwamnatin tarayya ta dakatar da amincewa da takaddun sha