An Kama Su Kan Tono Gawar Dan Maƙwabcinsu Domin Suyi Tsafi
An Kama Su Kan Tono Gawar Dan Maƙwabcinsu Domin Tsafi
Wasu mutane uku da suka tona kabarin dan maƙwabcinsu mai shekara daya a duniya suka yanke sassan jikin gawarsa sun shiga hannu.
’Yan sanda a Jihar Ondo sun gurfanar da mutanen su uku a gaban kotun Majastare ta garin Odigbo kan zargin su da tonon kabarin yaron da kuma yanke sassan jikin gawarsa domin yin tsafi.
Mai gabatar da kara, Mista James Usifom, ya shaida wa kotun cewa mutanen sun aikata laifin ne a ranaikun 5 da 9 ga watan Yuli da muke ciki a garin Omi-Ifon cikin Karamar Hukumar Odigbo.
Ya ce wata mata ce ta nemi taimakon malamai domin yin jana’izar gawar yaron dan shekara daya da take reno bayan rasuwarsa a asibiti.
Jami’in ya ce wadannan mutane uku da aka kama ne suka yi wa yaron jana’iza tare da binne gawarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Sai dai bayan kwana uku bayan binne gawar yaron ne matar da ’yan uwa da suke zaune a gida daya suka rika jin wani irin wari da ba su saba jin irinsa ba.
Hakan ne ya kai ga binciken da suka gano cewa daya daga cikin makwabtakansu da suka yi wa yaron jana’iza ya shafe daren wannan ranar yana daka wani abu a cikin turmi, kuna karar daka da doyin wannan abu ya hana su yin barci.
Bayan samun labarin sirri, matar ta kai kara zuwa ofishin ’yan sanda da suka kama wadannan mutane.
Binciken ya kai ga zuwa makabartar da aka binne yaron, inda da aka tono kabarinsa aka taras da an yanke kokon kansa da hannaye biyu.
Mai gabatar da kara, James Usifo ya ce binciken ’yan sandan ya tabbatar da cewa sassan jikin yaron da aka yanke ne maƙwabcinsu ya dake su a cikin turmi domin yin tsafi.
Ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba wa kundin Dokokin Jihar Ondo sashe na 517 da 516A(1), 242(1)(b),213(b).
Saboda haka ya roki kotun ta tsayar da dage sauraron karar domin ba shi damar yin bincike da samun tabbatattun shaidu da zai gabatar mata.
Amma James Usifo bai amince da bayar da belin wadanda ake tuhuma ba, saboda girman laifin da ake zargin sun aikata.
Lauya H.A. Ogiren da ke kare wadanda ake zargi, ya amince rokon mai gabatar da kara, amma ya nemi kotun ta bayar da belin su.
Alkalin kotun, Mai shari’a Festus Akinlolu, ya jingine bukatar neman belin zuwa ranar 26 ga watan Agusta mai kamawa
Comments
Post a Comment