An tsaurara matakan tsaro a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja yayin da ake shirin fara zanga-zangar yunwa a yau.

 Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnonin jihohin da gwamnatin tarayya suka yi kira ga masu zanga-zangar da su gudanar da zanga-zangar cikin lumana.



A Bauchi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Mohammed, ya ce rundunar ta tura jami’anta zuwa lungu da sako domin dakile karya doka da oda.

Jaridar Leardership ta ruwaito cewa rundunar ta bukaci masu shirya zanga-zangar da su baiwa ‘yan sanda cikakkun bayanansu suka hada da wuraren taro da hanyoyin zirga-zirga.


Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, ya raba wa manema labarai a Bauchi.


A nasa bangaren, kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Yobe, Adamu Idris Zakari, ya bayyana shirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar yayin zanga-zangar da ake yi a fadin kasar.


Zakari, wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ya bukaci jami’ai da matune da su rika gudanar da ayyukansu cikin kwarewa a yayin gudanar da ayyukansu.


Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta dauki matakin da ya dace kan dakile barna, sace-sacen jama’a, da sauran munanan ayyuka a yayin zanga-zangar da ‘yan kasa suka yi.


Da yake jawabi ga jami’an da aka tura a kananan hukumomin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello M Sani, ya shaidawa manema labarai cewa an tura sama da jami’ai 5,000 domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Tinubu Yana Kokarin Gaske Domin Tunkarar Kalubalai, Inji Sen. Barau

Gwamnatin Tarayya Ta Tsaurara Matakan Tsaro A Kan Iyakokin Kasar Gabanin Zanga-zangar Da Ake Shirin Yi A Fadin kasar Nan

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro domin tunkarar zanga-zangar adawa da wahalhalun da ake yi a fadin kasar, wanda aka shirya yi a cikin watan Agusta a jihar.